Daga Wakilin Mu
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa batun sanya jar hula ko rashin sanya jar hula ba shi ne muhimmin abinda ya kamata a mayar da hankali a kai a siyasa ba.
Sanata Shekarau ya ce koda mutum baya goyon bayan Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, dole ne a amince cewa ɗan siyasa ne, jagora ne kuma shugaba ne da ya taka muhimmiyar rawa a siyasar jihar Kano da Najeriya.
Haka Kuma ya ƙara da cewa kamar kowane ɗan adam, Kwankwaso ma baya rasa nasa kura-kurai da gazawa.
Shekarau ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai inda yayi tsokaci kan batutuwan siyasar da suka shafi Kano.










