Daga Hassan R Jibrin.


Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya jefi tsuntsu biyu da dutse daya irin na siyasa.
Alokacin wata ziyara ta neman tubarraki da ‘yan takarkarin gwamnonin jam’iyyar PDP daga jihohin Gombe, Bauchi,Kano a bisa jagorancin Mustapha Sule Lamido daga Jigawa, kuma da ga tsohon gwamnan, suka kai masa a gidansa dake garin Bamaina.
Yayin ziyarar ne ya yiwa Farfesa Isah Ali Pantami shagube inda ya cewa a baya
“ance PDP jam’iyyar barayi ce, kuna PDP jam’iyyar arnace”.
A bangaren gwamnatin Tinubu, kuwa yayi tsokaci dangane da alamun lalacewar harkokin gudanarwa, shugabanci da kuma mulkin Kasa,inda har Ma’aikatar ‘bogi’ ake da ita, mai ma’aikata har 300 dake karbar albashi a duk wata daga lalitar Gwamnatin Tarayya.
Ita dai wannan Ma’aikatar Saka Jari da Kare Muradun Gwamnati a Kasashen Waje ta Fadar Shugaban Kasa ( PFIPC) da ake ce-ce-ku-ce akanta, ana zargin ta bogi ce, duk da kasancewar Ofishin Sakataren GwamnatinTarayya na da hannu wajen samar mata da matsugunni a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya, dake Abuja da kuma bude mata shafin sadawar a hukumance da NITD mai alhakin yi, da kuma bude asusu a babban Bankin Kasa na CBN.
Farfesa Ali Pantami, a madadin takwarorin sa, ya godewa tsohon gwamnan yadda ya karbe su cikin
karimci, ya kuma kwatanta tsohon gwamnan da zama cikakken dan kishin talakawa, inda ya samu horo tun a bullar jumhuriya ta biyu, daga marigayi Malam Aminu Kano.
“Ban taba ganin tsohon gwamna yana zaune acikin talakawa kuma a kauyen da aka haife shi ba, in banda kai” a cewar Farfesa Ali Isah Pantami.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here