EDITA.
Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta shiga sabon takun-saka da Masarautar Zazzau bayan ta aika wa Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli, takardar gargaɗi ta hannun lauyoyin ta, inda ta nemi a buɗe mata masallatai takwas da aka rufe cikin kwanaki 30.
A cewar takardar, lauyoyin ƙungiyar sun yi zargin cewa rufe masallatan ya tauye haƙƙin mambobinta na gudanar da ibada, wa’azi da karantarwa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada. Sun kuma bayyana cewa idan ba a buɗe masallatan cikin wa’adin da aka bayar ba, ƙungiyar za ta ɗauki matakin shari’a domin neman hakkinta a kotu.
Rahotanni sun nuna cewa kwafin takardar gargaɗin ya isa ga manyan hukumomi da suka haɗa da ofishin gwamnan jihar Kaduna, rundunar ‘yan sanda, DSS da sauran jami’an tsaro domin sanar da su halin da ake ciki.
Lamarin ya fara jawo cece-kuce a tsakanin al’umma, inda wasu ke kallon matakin a matsayin gwagwarmayar kare ‘yancin addini, yayin da wasu ke ganin akwai buƙatar a warware matsalar ta hanyar tattaunawa domin kauce wa rikicin da zai iya haifar da rashin jituwa a tsakanin al’umma.
Yanzu dai idanu sun karkata ga Masarautar Zazzau domin ganin matakin da za ta ɗauka kafin cikar wa’adin kwanaki 30 da ƙungiyar Izala ta bayar. Wannan lamari na iya zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan addini da shari’a da za su ɗauki hankalin jama’a a Arewacin Najeriya a kwanaki masu zuwa.










