Daga Hassan R. Jibrin.

Ga dukkan alamu ga siyasar Najeriya na neman komawa bin tsarin jam’iyya daya. Dabarun amfani da karfin mulki da tursasawa ‘yan adawa yana bayyana a fili a sannu a sannu.

Babbar barazanar ga jam’iyya mai mulki ta APC, itace jam’iyyar hadaka ta ADC.

Baya ga zargin da akewa APC na kirkirar da kuma rura wutar rashin fahimta acikin ADC, da sauran jam’iyyun.

Duk da ADC na jiran samakon hukuncin Kotin Koli, ba tare da sanin takamaimiyar rana ba. Ita kuwa INEC, ta dade da sanar da ranar 18/05/2026 domin rufe karbar sunayen mambobin jam’iyyun Kasar.

Wasu na hasashen hukuncin zai iya zuwa ne a ranar 5/05/2026, bisa sharadin mayar da karar gaban wata Babbar Kotu.

Ranakun 6 da 7 duk babu aiki. Irin wannan kacimurda na siyasa ka iya dakushe fatan ADCn a zaben shekarar 2027.

Sauran jam’iyyun masu da’awar hamayya ka iya narkewa cikin jam’iyyar APC mai mulkin Kasar.

Koma meye, idan ba ayi hattara ba, jam’iyyar ADC gurguwa ce da auren nesa. Kuma ba zai yiwa siyasar Najeriya dadi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here