EDITA.
Hukumar Jin Dadin Alhazzai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da cewa, za a fara jigilar maniyyata daga Najeriya zuwa Kasa Mai Tsarki domin aikin Hajjin bana na shekarar 2026 a ranar 3 ga watan Mayu.
Tafiyar farko za ta tashi ne daga sabon Filin Jirgin Sama na Kasa-da-Kasa na Gateway da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, inda kamfanin jirgin FlyNas zai kwashe maniyyatan jihar. Wannan shi ne karon farko da maniyyatan Jihar Ogun za su tashi kai-tsaye daga jiharsu tun bayan gina filin jirgin.
Baya ga Jihar Ogun, sauran jiragen da za su tashi a wannan rana sun hada da Kamfanonin Umza da Max Air da za su kwashe maniyyatan jihohin Kogi da Nasarawa daga Abuja. Sai Kamfanin Air Peace zai kwashe maniyyatan Jihar Oyo daga Legas. Daga Birnin Kebbi, wani jirgin na FlyNas zai tashi da maniyyatan Jihar Kebbi.
Yayin da ake shirin fara jigilar, tuni jami’an NAHCON da suka hada da tawagar likitoci suka sauka kasar Saudi Arabiya a yau Talata, 28 ga watan Afrilu, domin yin shirye-shiryen tarbar maniyyatan Najeriya.
Hukumar ta fitar da wasu muhimman shawarwari kamar haka:
Tsarin Shiyya (Zones): Kowane kamfanin jirgi zai kwashe maniyyatan shiyya daya ne a lokaci guda. Da zarar an gama da shiyya aka koma gaba, jirgi ba zai sake dawowa wannan shiyyar ba. Duk maniyyacin da ya rasa jirginsa, zai dauki nauyin bin jirgin zuwa inda ya dosa ko kuma ya jira har sai an sake tsara tafiyarsa.
Tsarin Rukunin Mutum 45: Dole ne kowane maniyyaci ya yi tafiya a cikin rukuninsa na mutum 45.
Katin Nusuk na maniyyata suna nan a shirye suna jiran isowarsu Saudi Arabiya.
Ana shawartar maniyyata su san sauran mambobin rukuninsu, sannan su tanadi lambobin wayar shugabannin rukuninsu da na jami’an jihohinsu.
Shugaban hukumar NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya ba wa maniyyatan kasar tabbacin cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da an gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin nasara da sauki.
A halin yanzu dai, maniyyata na ci gaba da shirin karshe na bankwana da iyalansu gabanin fara fita zuwa filayen jirgi a mako mai zuwa.










