Daga Hassan R Jibril.


Rade-raden da akeyi na sauya shekar tsohon dan-takarar gwamna a zaben 2023 a jam’iyyar NNPPn jihar Jigawa,Mallam Aminu Ibrahim Ringim ya zo karshe.
Magoya baya a ciki da wajen jihar ne suka shaida sauyen shekar dan-siyasar.
Idan za’a iya tunawa Mallam Aminu yana daga cikin gyauron ‘yan siyasar jumhuriya ta biyu, a inda ya taba zama wakili a majalisar wakilai ta tarayya.
Komawar ta sa,wani Karin jarfi ne ga jam’iyyun adawa a jihar ta Jigawa,sai dai abin lura shine ko burinsu na kawo karshen gwamnatin APC ta Mallam Umar Namadi zai Kai ga cika. Lokaci ne kadai zai nuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here