EDITA.
Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa da su riƙa ba masu amfani da layi diyya ta hanyar saka musu katin kuɗin waya idan suka samu matsalar rashin ingancin sadarwa na rashin sabis.
Shugaban NCC, Aminu Maida, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Lagos, inda ya ce an ɗauki matakin ne bayan an tabbatar da cewa wasu kamfanoni sun gaza cika ƙa’idojin ingancin sabis a wurare da dama.
Ya jaddada cewa wannan ba wani kuɗin mayarwa daga gwamnati ba ne, illa wajibi ne da aka ɗora wa kamfanonin sadarwa su cika.
A cewarsa, dole ne kamfanonin su ɗauki alhakin duk wata matsala da ta shafi sabis ɗin su.




