Hassan Turaki.

Ana iya yin su a kowane lokaci cikin watan Shawwal:
• a farkon wata,
• a tsakiyar wata,
• ko a ƙarshen wata.

Haka kuma, ana iya yin su:
• a jere,
• ko a rarrabe.

Ko da kafin ka rama azumin da ka bari, ko bayan ka rama — duk yana da falala.

Manzon Allah (SAW) ya ce:
“Duk wanda ya yi azumin watan Ramadan, sannan ya bi shi da azumin kwanaki shida na Shawwal, kamar ya azumci shekara ɗaya ne.”

Dalili kuwa shi ne: kowane aikin alheri ana ninka ladansa sau goma.
Saboda haka, kwanaki 30 na Ramadan su zama 300, sannan kwanaki 6 na Shawwal su zama 60 — jimilla 360, daidai da kwanakin shekara.

Allah Ya ba mu ikon aikata wannan falala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here