EDITOR.

An shiga yanayin fargaba a cocin St. Matthias Catholic Church da ke Agulu, a ƙaramar hukumar Anaocha ta jihar Anambra, bayan da wata babbar motar kaya (lorry) ta daki ginin cocin sannan ta kama wuta nan take.

Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba, inda aka bayyana cewa direban motar yana gudu sosai, sai ya kasa sarrafa motar a kan gangara, wanda hakan ya sa ya faɗa cikin shingen cocin.

Bayan bugawar ne wuta ta kama motar. Duk da girman hatsarin, ba a rasa rai ba kuma babu wanda ya ji rauni, sai dai direban motar ya tsere daga wurin da zaran hakan ta faru.

Lamari ya haddasa cunkoson ababen hawa a hanyar Agulu zuwa otal ɗin Golden Tulip, yayin da mutane da jami’an agaji suka yi ƙoƙarin kashe wutar kafin zuwan jami’an kwana-kwana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here