Daga Hassan R Jibril.
Rahotanni na nunin cewar jam’iyyar APC a jihar Katsina na shirin bude wani babin rikici a Kananan Hukummomin Daura,Sandamu da Mai’adua.
Wasu ‘ya’yan jam’iyyar da suka hada da Shugaban Karamar Hukumar Daura da sauran jiga-jigan APCn, sun yanke shawarar tsayar da dan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari takarar majalisar Tarayyar, yayin da wasu bangarorin suka yi fatalli da shirin.
Acewar masu bukatar, wakilin dake a yanzu ka ‘iya neman kujerar Sanata.
Wasu wakilan Kananan Hukummomin biyar tuni su ka nuna adawar su a fili.
Kamar yadda wasu ke ganin Yusuf Buhari ya samu karbuwa acikin talakawan yankin, kuma da irin gudummawar da yake bayarwa ga siyasar yankin na Daura, hakan na iya zama tukuici a siyance.










