Daga Hassan R Jibrin

Shugaban tsofaffin daliban makarantar firamare aji 1981 da ke garin Gano a Karamar Hukumar Dawakin-Kudu a jihar Kano, Dr Tijjani Yahaya ya bukaci karin hadin kan masu ruwa da tsaki a harkar ilmi da su kara bada gudunmawa don bunkasa ilmi a yakin nasu.

Kiran na kunshe ne yayin gudanar da taron kungiya.’Ya’yan kungiyar daga bangarori daban-daban suka halarta.

Yayin taron, an karrama Injiya Yahaya Muhammad Odiye, da shaidar girmawawa ta kammala shekaru 35 na aikin gwamnati da kuma yi masa jinjina ga ire-iren gudunmawar da ya bayar ga cigaban yankin a fannoni daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here