Daga Hassan R Jibrin
Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano bisa umarnin gwamnatin jiha, ta sanar da rufe makarantu daga ranar Juma’a 22 ga watan Mayu zuwa Litinin 1 ga watan Yuni ga makarantun jeka,-ka-dawo.
Su kuma makarantun kwana daga ranar Juma’a 22 zuwa Lahadi 31 ga Watan Mayu.
Sanarwar ta shawarci iyayen yara da masu kula da su, su tabbatar yaran makarantun kwana sun koma a ranar da aka labarta da kuma zuwa makarantun domin daukar ‘ya’yan nasu.










