Daga Hassan R. Jibrin.
Darakta-janar na Cibiyar Kula Da Cuttuka Masu Saurin Yaduwa ta Kasa, Mr Jide Idris ya shaidawa manema labarai cewar, kawo yanzu cutar Ebola bata shigo Najeriya ba.
Cibiyar tayi wani shirin ko-ta-kwana dangane da cutar.Hukumar Lafiya ta Duniya ce ta sanar da bullarta a Kasar Jumhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a watannin da suka gabata.
Zubar jini ta kafofin idanu da kunnuwa na daga alamunta ga wanda ya kamu,kuma tana saurin yaduwa da kisa a kankanin lokaci.
Ana alakanta cutar da cin naman biri da wasu dabbobin daji.










