Abubakar Salihu.
Wata babbar Kotun Jihar Gombe mai lamba 2 ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi mai shekaru 18, Mustapha Adamu Isah, wanda aka fi sani da Abbati, bayan ta same shi da laifin kashe wata mata mai shekaru 58 mai suna Aishatu Abdullahi, wadda aka fi sani da Damori.
Mai shari’a Abdulhamid Mohammed Yakubu ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba.
Kotun ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 20 ga Oktoba, 2023, da karfe 9:00 na dare a unguwar Jekadafari da ke Gombe.










