Jafaru Ibrahim.
Wasu fusatattun direbobin manyan motoci sun rufe hanyar zaria zuwa kaduna a daidai marabar jos.
lamarin ya faru ne sakamakon rikici da wani direban babbar mota ya yi da jami’an hukumar KASTLEA, inda suka rutsa shi a garin Maraban Jos suka cire masa batirin mota.
Haka kuma, an tattaro cewa direbobin sun dakatar da zirga-zirgar motoci a wannan hanya har sai an sasanta rikicin.
Idan ba’a manta ba, ko a watannin baya an samu makamancin irin wannan rikicin tsakanin direbobin manyan motocin da jami’an KASTLEA.










