Ibrahim A. Makama.
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin wanda zai yi hawan Sallar bana.
Idan za a iya tunawa dai, a makon jiya ne Aminu Ado Bayero yayi riga malam masallaci ya sanar da ƴan sanda shirin sa na gudanar da hawan sallah.
Wasu daga cikin masana harkokin tsaro na ganin cewa gwamna da gwamnatin jihar kano ce tafi dacewa da bada umarnin hawan sallah ga sarki a kowace jiha, kamar yadda bada tsaro a yayin hawa yake rataye a wuyan jami’an tsaro a mataki daban-daban.










