Yakubu Uba Muhd.
Gwamnatin Bauchi ta sallami wani direbanta bayan ya yi haɗari da mota har ‘yan jarida biyu suka rasu.
Gwamnatin jihar Bauchi ta kori direban ne bayan tabbatar da cewa sakacin sa ne ya haddasa haɗarin mota mai muni da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan jarida biyu da ke bakin aiki.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne yayin da wadanda abin ya shafa ke gudanar da aikin su na yada labarai lamarin da ya jefa al’umma cikin matsanancin jimami.










