Daga Hassan R Jibrin.

Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Muhammad Sama’ila Mera CON, ya umarci al’ummar masarautar sa da su fara tunanin mallakar makamai ta hanyar da dokar Kasa ta shimfifa domin kare kansu daga hare-haren ‘yan ta’adda.

Sarkin ya bada umarnin ne, a fadarsa yayin wani taro da hakimai, dagatai da masu unguwanni da sauran masu rike da mukaman sarautun gargajiya. Taron yayi duba ne ga yankin masarautar ke fuskanta.

Ya kuma yi gargadin cewa, mallakar makamai ba hujja ba ce yin amfani dasu wajen aikata ba dai-dai ba, yin hakan ya sabawa dokar mallakar su.Jihar Kebbi, daya ce daga jihohin Arewa maso Yamma, inda ‘yan ta’adda ke cin karensu babu babbaka, ta hanyar fashin daji da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here