Hassan R Jibrin.
Bayan sauya shekar tsohon Ministan Tattalin Arziki na Zamani, daga jam’iyyar APC zuwa PDP, Farfesa Ali Isah Pantami ya samu damar takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP.Tsohon Ministan, ya shiga zawarcin kujerar gwamna a AP, hakansa bai cimma ruwa ba biyo bayan zargin magudi da nuna goyon bayan wani dan-takarar daga bangaren gwamnatin jihar ta Gombe.










