Daga Hassan R Jibrin
Kotun Kolin Najeriya ta yanke hukunci akan rikicin cikin gida dake addabar shugabancin jam’iyyar ADC a Nigeria.
Bisa doron hukuncin da kotun kolin tayi, Sanata David Mark, shine halastaccen shugaban jam’iyyar ta ADC ba abokin burmin sa ba Alhaji Nafi’u Bala Gombe.
Haka Kuma hukuncin kotun ya tabbatar da shari’ar dake gaban Babbar Kotu. domin cigaba da sauraro.
Wannan hukuncin shine ya balle makatar da INEC ta dogara wajen soke sunayen shugabanin tsagin Sanata David Mark.










