Daga Hassan R Jibrin.

Jam’iyyar NDC reshen jihar Kano, tayi kira ga gwamnatin jiha da ta zage damtse wajen dakile fadace-fadacen daba da kwacen wayoyi.

A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar a Kano, Mallam Yusuf Fasaha ya fitar ta shafin sa na Facebook, ya nuna takaici ta ganin fadan daba na neman dawowa.

Ya kara da cewa lamarin ba zai haifarwa jihar da mai ido ba a fannonin tattalin arziki da zamantakewa.

Ko a ranar da ake gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, wasu gungun matasa dauke da muggan makamai sun farwa junansu a unguwar Kofar Wambai.

Shedun gani da Ido sun tabbatar da cewa fadan tsakanin unguwar Fagge ne da Kofar Wambai da wasu daga unguwar Zage a inda suka jiwa junan su rannuka iri daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here