EDITA.
Masanin yada labarai kuma me sharhi kan harkokin siyasa, Dele Momodu, ya bayyana cewa yana da cikakkiyar tabbacin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na daga cikin mutanen da ke da ƙarfin fafatawa a zaben shugaban ƙasa na 2027.
Da yake magana a wata hira da yayi da tashar News Central TV, Momodu yace sakamakon zaben 2023 ya nuna cewa yanayin siyasar Najeriya na iya haifar da abubuwan da ba’a zata ba, musamman a yadda mutane ke kada ƙuri’a a yankuna daban-daban na fadin Kasar.
Ya nuna yadda ɗan takarar Labour Party, Peter Obi, yayi ƙarfi a Jihar Legas a matsayin misali na sauyin dake faruwa a siyasa. A cewar sa, sakamakon da Obi ya samu a 2023 ya baiwa mutane mamaki kuma ya sauya tunanin da ake da shi game da yadda yankuna ke kada ƙuri’a.
Momodu ya kuma ambaci yadda Atiku Abubakar yayi ƙarfi a Jihar Osun, yana mai cewa hakan wata alama ce dake nuna cewa yankunan da ake ganin sunfi kowa ƙarfi a siyasa ba su kasance masu tabbata ba kamar da.
A cewarsa, siyasar Najeriya na canzawa cikin sauri dangane da yanayin ƴan takara, haɗin gwiwa, da kuma yanayin ƙasa baki ɗaya.
Ya kara da cewa idan Peter Obi ya sake tsayawa takara a 2027, zai iya ci gaba da samun goyon baya mai ƙarfi a Kudu maso Gabas, inda har yanzu shaharar sa ke da girma.
Momodu ya kuma ambaci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin wanda zai iya zama mai ƙarfi a Kudu maso Kudu idan ya sake komawa takara, yana mai cewa Jonathan har yanzu yana da mutunci a wasu sassan ƙasar.
Bugu da ƙari, ya ce Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, zai iya yin tasiri a yadda mutane ke kada ƙuri’a a Kudu maso Yamma, ganin yadda matsayin sa na siyasa ke ƙaruwa da kuma shaharar sa a matakin ƙasa.
Duk da haka, Momodu ya jaddada cewa duk da waɗannan mutane, Atiku Abubakar ne har yanzu ɗan siyasar Arewa dake da ƙarfi kuma yana da tasiri a faɗin ƙasar nan.









