Muhammad Chamama.


Akwai yiwuwar Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, zai yi murabus daga mukaminsa a kowane lokaci.


Wannan rahoto na zuwa ne bayan wasu alamu da ke nuni da rashin daidaito a yadda ake tafiyar da wasu al’amura a jihar, musamman dangane da batun tarbiyya da kula da ɗabi’un al’umma.


Majiyoyi sun bayyana cewa, Malam Daurawa na iya ɗaukar wannan mataki ne sakamakon yadda yake ganin ba a ba shi cikakken goyon baya wajen gudanar da aikin sa na gyaran tarbiyya, musamman a wasu lamura da suka shafi ɗabi’a da ladabi a cikin al’umma.


Idan ba a manta ba, a baya Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya taɓa samun saɓani da gwamnatin jihar Kano kan wata ‘yar TikTok da aka fi sani da Murja Kunya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a tare da tada muhawara kan yadda ya dace a tafiyar da batutuwan tarbiyya da ‘yancin kai.


Masu sharhi na ganin cewa, irin wannan yanayi na iya shafar yadda hukumar Hisba ke gudanar da ayyukanta, musamman idan aka ci gaba da ganin wasu na aikata abubuwan da suka s

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here