Hassan Turaki.
Hon. Ahmad Isah Barayan Dutse Dan takaran Sanatan Jigawa ta tsakiya a karkashin tutar jam’iyyar ADC, yayi wannan ikirari ne yayin ganawar sa da manema labarai a gidan sa dake birnin Dutse.
Jam’iyyar ADC a jihar Jigawa kamar kowacce jiha ta aiwatar da tantance yan takaran Sanata na kowani shiyya kamar yadda uwar Jam’iyyar ta kasa ta sahale musu.
Da yake amsa tambayar yan jarida dangane da yadda jam’iyyar sa ta tantance shi, Baraya ya kada baki yace; ya gabatar da dukkannin takardun sa da kwamitin tantancewar ta bukata Kuma anyi komai an kammala ba tare da wata matsala ba.
“Duk wata takarda da nasa a fom na nuna wa kwamitin tantancewa sahihiyar ta” Inji Baraya.
Dan takaran Sanatan Jigawa ta tsakiya ya kara da cewa a shirye yake ya fara yawon neman kuri’un masu zabe da zarar lokaci yayi domin gabatar da kan sa da Kuma sanin matsalolin su kasancewar a shirye yake ya maganace musu idan suka bashi dama.
Yace zai bada fifiko a ɓangaren lafiya da noma da hanyoyi domin hanya na tallafa wa harkokin noma sai Kuma ɓangaren ruwan Sha da ilimi.Ya koka dangane da dumama kijera irin na Sanatan Jigawa ta tsakiya da Kuma Dan majalissar tarayya me wakiltar Dutse da Kiyawa a majalissar tarayyar kasa, inda yace basu yi wa mutane abinda ya dace ba.
Ahmad ya kara da cewa idan ya samu dama zai duba asibitocin gwamnati domin ganin abinda zaiyi don farfado dasu.
Dan takaran Sanatan Jigawa ta tsakiya a karkashin tutar jam’iyyar ADC yace rashin temakon matasa da kananan jari a matakin farko shine yasa basu iyan yin abinda ya dace a ɓangaren kasuwanci har takai suna iya fita jihohi domin yin kasuwanci.
Ahmad ya nuna rashin gamsuwar sa dangane da ɓangaren aikin ruwa da lafiya, inda yace yawancin aiki ne na gangar baka, “abinda gwamnati take cewa tayi daban da abinda talaka yake gani” Inji shi.
A karshe yace a shirye yake ya sanya hanu domin bada gagarumar gudumawa kan duk wani aiki da gwamnatin jiha za tayi domin alu’mar yankin ta amfana.










