Ibrahim A. Makama.
Sanatan Kano ta Arewa, Sanata Barau I Jibril ya bayyana cewa ya halarci tantancewar jam’iyyar APC ga masu neman takarar Sanata a Abuja, kwanaki biyu bayan mika fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara domin sake neman kujerarsa.
a sanarwar da ya wallafa, ya ce bayan samun nasarar tantancewar, zai sake neman amincewar al’ummar Kano ta Arewa domin ci gaba da wakilcinsu tare da dorewar ayyukan ci gaba da ake gudanarwa a mazabar Sanatan.
Ya bayyana cewa zai ci gaba da jajircewa wajen kawo ƙarin ci gaba da inganta rayuwar al’umma, yana mai cewa siyasa a wajensa hanya ce ta hidimtawa jama’a da samar da walwala.
Sanatan ya kuma gode wa al’ummar Kano ta Arewa bisa goyon bayan da suke ba shi tsawon shekaru, yana mai bayyana fatan cewa a zaɓen ranar 16 ga Janairu, 2027, al’umma za su sake sabunta masa amanar wakilci domin ci gaba da bunƙasa tattalin arziki da ci gaban yankin.










