Daga Hassan R Jibrin.

Kamar yadda alamun iskar siyasar yankin Kano ta kudu ke kadawa, Sanata Kawu Sumaila na shirin sabon karatu a babin siyasar yankin na su.

Hakan na zuwa ne yayin da Shugabannin kananan hukumomin yankin su sha shida, suka amince da nuna goyon baya da kuma marawa tsohon shugaban majalissar dokokin jihar Kano kuma wakilin Rano, kibiya da Bunkure, Rt Hon. Kabiru Alassan Rurum domin takarar sanata a zaben 2027.

Wannan sauyin lamuran siyasar, wasu na ganin yana da alaka da irin rawar da Sanatan ya taka a takaddamar fitar da mataimakin gwamna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here