Daga Hassan R Jibrin

Tsohon dan takarar Shugabancin Karamar Hukumar Dawakin-Kudu a jihar Kano, Alhaji Bashir Inuwa Dawakiji, ya yi kira ga al’ummar musulmai da su hada kawunansu a duk inda suka tsinci kansu domin hadin kai tubalin samun daraja ne agare su.Ya bada wannan shawarar ne yayi walimar da Kungiyar Da’awah ta garin Gano dake Karamar Hukumar Dawakin-Kudu domin murnar taya daya daga cikin limaman garin, Sheik Yusuf Ibrahim dangane da auren da yayi.Ya kuma kara nuna jin dadin sa tare da ganin sun kara jaddada kyakkyawan hadin kai a tsakanin malaman mabanbanta dariku.Akalla malamai da daliban ilmin addinin musulunci kusan sama da arba’in suka halarci taron walimar a babban masalallacin juma’ar. garin na Gano. Taron ya samu halarta daga jami’an tsaron yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here