Daga Hassan R. Jibrin.


Shugaban Hukumar Alhazai Ta Kasa, Ambassada Isma’il Abba Yusuf, ya umarci sashen tsaro na hukumar da ya binciki yadda aka baiwa alhazan Najeriya abinci mara inganci a ranar talata.

A cewar Hukumar, abincin bai cika ka’idar da hukummomin Saudiyya suka gindaya ba.
Ya kuma tabbatar da ganin an hukunta masu laifin.

Rashin ingancin abincin a wannan rana, ya janyo baiwa alhazan wani nau’i na daban kamar leman robobi da makamantansu.


Baya ga binciken abinci, Hukumar zata kuma binciko yadda kamfanonin zirga-zurga suka zarce yawan alhazan da aka yarje musu domin kawowa aikin hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here