Daga Hassan R Jibrin.
Biyo bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, wata kungiyar jam’iyyar ta Arewa ta Tsakiya karkashin Alhaji Saleh Zazzaga ta umarci shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Natwe da ya gaggauta yin murabus nan da sati biyu.
Kungiyar ta zargi shugaban ne da tatsar makudan kudade daga masu sha’awar takara da kuma chanja sakamakon zabe da kuma hana wasu shiga takara.
Alhaji Saleh ya kuna nuna bacin ran kungiyar da cewar kaso hamsin basu gamsu da yadda aka gudanar da zaben a karkashin shugaban ba. Ya kara da cewar, idan har shugaban bai sauka daga jan ragamar jam’iyyar ba, a shirye Kungiyar ta garzaya gaban kuliya domin ceto APC daga badakala’ar da aka jefa ta domin biyan bukatar wasu ‘yan tsiraru.
Hakan tamkar wani arashi ne ,akan yadda wasu Gwamnonin APC suka nuna damuwarsu kan shugabancin jam’iyyar alokacin tantace ‘yan rakarkari.










