Hassan R. Jibrin.
Fadar Mai Martaba Sarkin Ringim, a jihar Jigawa ta fitar da sanarwa bisa umarnin Sarkin, Alhaji (Dr) Sayyadi Abubakar Mahmud Usman CON, da a gudanar da sallar rokon ruwa da kuma azumin kwanaki uku domin nreman afuwar Ubangiji da kuma ganin karshen karancin saukarruwan sama.
Ana sa ran gudanar da addu’o’in ne, a babban masallacin idin garin na Ringim a safiyar Laraba. Matasa, dattawa da kuma tsofaffi da sauran al’ummar garin na Ringim da kewaye, ake sa ran yin dandazo domin biyayya ga umarnin masarautar.Ko a kwanakin baya, masarautar ta fitar da irin wannan umarnin ba tare da gudanar da sallar ta rokon ruwa ba.
Damina a yakin masarautar ta yi kamfa matukar gaske, hakan na nufin da yiwuwar wata barazanar samun karancin cimaka a kakar badi, idan ba Allah ne ya kawowa al’ummar dauki na musamman ba.










