Hassan Turaki.
Ana zargin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru el-Rufa’i cewa, ya ba da takardun shedar rashin lafiya na ƙąrya domin a ba da belin sa.
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta sake yin watsi da buƙatar neman belin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya shigar a cikin shari’ar laifuka da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa da Hakan (ICPC) ta shigar a kansa.
Mai Shari’a Darius Khobo ne ya yanke wannan hukuncin a kan buƙatar neman belin wanda ake ƙara na uku, wanda a wannan karon aka dogara da dalilai na lafiya.
Kotun a wannan karon ta bincika rahoton lafiyar da Mallam Nasiru El-Rufai ya dogara da shi domin mara wa bukatar sa baya.
Rahoton, wanda aka nuna cewa Babban Asibitin Ƙasa da ke Abuja (National Hospital) ne ya fitar da shi, ya yi ikirarin cewa an gano tsohon gwamnan yana ɗauke da cutar daji ta mafitsara (prostate cancer) wadda ta riga ta bazu, kuma tana buƙatar kulawa ta musamman, wadda aka ce babu irin ta a ko’ina a cikin Najeriya.
Yayin da take kalubalantar wannan buƙatar, hukumar ICPC ta gabatar da hujjoji na takardu daga Babban Jami’in Gudanarwa na Babban Asibitin Ƙasa na Abuja, Farfesa Muhammad Raji Mahmud, inda ya ƙaryata takardar da wanda ake ƙara ya dogara da ita.
Bisa ga takardar da ta fito daga Babban Asibitin Ƙasa, wadda Babban Jami’in Gudanarwa na asibitin ya sanya wa hannu, bincike mai zurfi da aka yi a cikin bayanan na’ura mai ƙwaƙwalwa na asibitin da jerin sunayen marasa lafiya, ya nuna cewa babu lambar asibiti, babu fayil ɗin mara lafiya, babu bayanan biyan kuɗi, babu tarihin duba shi, ko wata shaida da ke nuna cewa an taɓa yi wa wanda ake ƙaran magani a asibitin.
Haka kuma, asibitin ya tabbatar da cewa an fitar da rahoton ne ba tare da saninsa ko amincewar hukumar gudanarwar asibitin ba.
Da take dogaro da wannan shaida, Kotun ta bayyana cewa gaskiya da ingancin rahoton lafiyar sun gurbace kacokaf, kuma takardar da hukumar da aka yi amfani da sunanta ta fito fili ta ƙaryata ta ba za ta iya zama harsashin ba da wani babban rangwame da mai neman belin yake buƙata ba.
Sakamakon rushewar hujjojin, Kotun ta tarar cewa babu wasu hujjoji na gaskiya tabbatattu daga ingantacciyar hukuma da za su ba ta damar yin amfani da ikon da doka ta ba ta don amincewa da belin bisa dalilan rashin lafiya.
Dalilin haka, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar, kuma ta ba da umarnin cewa dole ne Hukumar (ICPC) ta ci gaba da ba wa wanda ake ƙara dama ba tare da takaitawa ba don ganawa da likitocinsa na kashin kansa, sannan ta tabbatar da cewa an raka shi zuwa kowace cibiyar binciken lafiya ko asibiti na musamman da yake so a cikin Najeriya kamar yadda buƙata ta taso, a tsawon lokacin da ake tsaka da gudanar da shari’ar.










