Daga Hassan R Jibrin
Kimanin ‘yan Mata dari da biyar (105) ne suka haddatace Al’kur’ani Mai tsarki a jihar Enugu dake Kudu maso gabashin Najeriya.
Wannan samun cigaban da addinin musulinci keyi a sassan Kasar ba abun mamaki bane duba da jajircewar iyaye da malamai wajen yada addini musulunci a cikin al’uma.
Duk da cewar wasu nayiwa addinin na musulunci mummunar fahimta, hakan bai hana addinin musulunci ratsa sassan Kasar ba.
Taron Yaya daliban ya samu halartar manyan malaman addinin musulinci ‘yan asalin kabilar Ibo (Iyamura).










