Abdullahi Aminu Jahun.

Kwamitin Zakka da Waqafi na jihar Jigawa ya kawo ziyarar aiki ga Gidauniyar Waqafi ta karamar hukumar Jahun a ranar Litinin.

Sakataran kwamitin Amintattu na Gidauniyar Waqafi ta Jahun, Alhaji Salisu Abubakar ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabin maraba ga wakilan kwamitin karkashin jagorancin Sa’in Dutse, Dr Mahmud Yunus, a Dakin karatu dake Jahun.

Alhaji Salisu Abubakar ya bayyana irin tsare-tsaren da suke gudanarwa dangane da kaddamar da Gidauniyar Waqafin, inda ya bayyana cewa suna kan tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin wayar da kawunan su kan tsarin Waqafi a Addinin muslunci.

Shima a nasa jawabin, mamba a kwamitin, Alhaji Ghali Iguda, ya bayyana irin nasarori da aka samu dangane da tsare-tsaren kafa Gidauniyar, inda ya bayyana cewa Kwamitin ya tsara gudanar da bita ga masu ruwa da tsaki a Gundumomin Hakimai Hudu da ake da su a karamar hukumar Jahun wanda tuni kwamitin ya fara gudanar da bitar a Gundumar Hakimin Jahun.

Tunda farko, a jawabinsa, jagoran wakilan kwamitin Zakka da Waqafi ta Jihar Jigawa, Dr Mahmud Yunus, ya bayyana jindadinsa dangane da yadda ake tafikar da tsare-tsaren, inda ya kuma bayyana makasudin ziyarar domin sanin matsayar da ake dangane da tsare-tsaren kaddamar da Gidauniyar Waqafi ta karamar hukumar Jahun, tare da bada shawarwarin da suka dace wadanda za su kai ga nasara.

Dr Mahmud Yunus ya kuma bukaci da a samar da kananan kwamitoci tare da sanya nagartattu da Amintattun mambobin, inda ya kuma yi kira da a samar da hadin kai na gaba daya domin kada a bar wata kafa da za ta samar da husuma ko rashin jituwa a tsakanin mambobin kwamitin wanda hakan zai iya rusar da kyakkyawan tsarin gudanar da Gidauniyar.

A jawaban su daban daban, wakilan mambobin Kwamitin Zakka da Waqafin, Malam Yakubu Muhammad Auyo, da Malam Ishaq Hussaini Muhammad, sun karfafa da a ci gaba da wayar da kan masu ruwa da tsaki a sauran Gundumomin Hakimai Uku da suka rage a karamar hukumar, tare da sanya lokacin da za a kaddamar da Gidauniyar Waqafin na karamar hukumar, inda suka jaddada cewa shirye-shiryen da kwamitin ke gudanarwa ya dauki kaso 80 cikin 100.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here