Daga Hassan R Jibrin.
Shahararren jarumin Bollywood dake Kasar Indiya, wanda ya fito daga lardin Tamil Nadu mai suna Jai, ya sanar da rungumar addinin Musulinci.
Jarumi Jai ya ce shigar sa addinin ya biyo bayan nazari mai zurfi ta hanyar kai ziyarce-ziyarce wuraren addininai mabanbanta domin mafita.
“A duk inda na je sai masu bauta su mamaye ni domin yin hoto da ni.
Amma a masallatai ne kawai babu wanda ya damu da ni domin sun karkata wajen yin bauta kawai. Wannan ta sa na gamsu da cewa addinin musulinci shine mafi nagarta” inji jarumi Jai.
Addinin musulunci sai kara karbuwa yake a sassa daban-daban na duniya, musamman a kasashen Amurka Tarayyar Turai da kuma Koriya ta Arewa.










