Daga Hassan R Jibrin.
‘Yan-sanda a jihar Yobe sun damke wani matashi mai suna Kamaluddeen bisa zargin badda kama wajen kutse acikin gidan wata budurwa.
Wanda ake zargin, yana shigar mata ne domin aikata wani boyayyen laifi.
Iyayen budurwar sun nemi a sakaye sunansu dana ‘yar tasu.
Tuni dai jami’an ‘tsaro suka dukufa wajen binciken akan lamarin domin gaggauta gurfanar da shi a gaban kuliya.










