By Engr. Qareebullah

Dan gwagwarmayar kare hakkin bil’adama kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya bayyana rashin amincewarsa da Sashen IGP Monitoring Unit na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya wajen gudanar da bincike kan bacewar da kuma zargin kashe Dadiyata.

Sowore ya ce ba zai yiwu a dogara da sashen wajen gudanar da bincike mai zaman kansa kan manyan ‘yan siyasa da masu fada a ji da ake zargin suna da alaka da lamarin ba.

Saboda haka, ya bukaci a kafa Kwamitin Binciken Shari’a domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.Ya kuma nemi a gayyaci tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, tsohon Darakta Janar na DSS Yusuf Bichi, tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, da kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya Abubakar Malami domin amsa tambayoyi kan zargin hannu a lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here