Ibrahim A. Makama
Jami’an tsaron farar hula ta (Civil Defence) a jihar Kano sun samu nasarar kama wani mutum mai suna Suleiman M. Uba sanye da bindigogi kirar gida guda shida (6).
Jami’an sun kama shi ne yayin sintiri a kan titin Murtala Muhammad dake cikin birnin Kano. Wanda Aka Kama me suna Suleiman mai shekaru 31, ɗan asalin garin Tashene ne a jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa yana kan hanyar sa ta zuwa jihar Kebbi ne lokacin da asirin sa ya tonu.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar a Kano, Ibrahim Idris Abdullahi, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kuma za’a gurfanar da shi a gaban kotu da zaran an kammala.










