Abdulaziz Muhammad Hadejia.
A yammacin ranar Asabar ce gobara mai tsanani ta tashi a wajen sayar da iskar gas ta girki da ke kan hanyar Katagum, cikin garin Hadejia, jihar Jigawa, lamarin da ya jawo tashin hankali a cikin al’umma.
Wakilinmu, Abdulaziz Muhammad Hadejia, ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a wani shagon sayar da gas, daidai lokacin da wata motar dakon gas ta isa shagon domin sauke sabbin kayayyaki.
Bisa bayanan da wakilinmu ya tattara daga wurin, hatsarin ya samo asali ne sakamakon yin suyan awara a wani wuri da ke kusa da shagon. Wutar da ake amfani da ita ta taba iskar gas, abin da ya haifar da fashewar gobarar cikin sauri.
Ganin yadda wutar ta karu cikin kankanin lokaci, dubban mutane suka taru a wurin cikin firgici, yayin da wasu ke kokarin ceto kayansu daga shagunan da ke makwabtaka da wurin.
Tuni jami’an tsaro da jami’an kashe gobara suka dira wurin domin daidaita martani da kuma shawo kan lamarin. Haka kuma sun kare lafiyar mutane da kuma hana wutar bazuwa zuwa wasu shaguna.
Wani mazaunin garin da ya shaida lamarin ya ce “mun ji kara kamar fashewar bama-bamai” lokacin da bututun gas ke fashewa daya bayan daya. Ya ce yanayin ya cika da hayaki mai yawa da kuma tsoro.
Alhamdulillah, bisa ga rahoton farko, ba a samu asar rayuka ba a cikin wannan hatsari. Wannan ya samo asali ne saboda kasancewar mutane sun gudu da wuri bayan ganin farawar wutar.
Duk da haka, wutar ta yi barna mai yawa ga dukiyoyi. Shagon da abin ya shafa gaba daya ya kone tare da kayayyaki masu yawa na iskar gas da sauran kayan kasuwanci.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a tantance adadin asar da aka yi ba. Amma shaidun gani da ido sun ce asar ta kai miliyoyin Naira. Sama da bututun gas guda 10 ne suka fashe gaba daya yayin gobarar.
Al’umma na ci gaba da kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su tsaurara ka’idojin tsaro a wuraren sayar da gas, da kuma hana yin duk wata harkar da ta shafi wuta kusa da shagunan gas domin gujewa afkuwar irin wannan hatsari nan gaba.










