DAGA: Hassan Turaki.
Kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Jigawa SP Shi’isu lawan Adam ya shaida mana;
Hedikwatar Yan Sandan Jihar Jigawa ta cimma manyan nasarori cikin sa’o’i 48, inda ta kama wanda ake zargi da zargin sace-sace bara, sannan ta rushe wata kungiya ta ‘yan satan baburori a Kazaure
Shi’isu yace Jami’an Sashen Takur Site, bisa sahihin bayanin sirri, sun kama Mustapha Umar, dan shekara 19, na Karamar Hukumar Azare, Jihar Bauchi, a ranar 22 ga Watan Yuni, 2026 da karfe 12:00 na rana, bisa zargin satar wayar salula ta Samsung A14 wacce ta mallaki Mercy Onoja.
A lokacin bincike na farko, wanda ake zargin ya amsa cewa ya hada Kai ne da wasu abokan aikin sa guda uku da ke Jihar Kaduna da Bauchi wadanda yanzu haka suke tserewa.
Bincike da aka yi a dakin su na otal ya kai ga samun wasu muhimman abubuwa. Abubuwan da aka gano sun hada da wuka, mabuɗan sirri, screwdriver, almakashi, kararrawa, turare, agogon hannu, wayar salula, da sauran kayan aikin da ake zaton ana amfani da su wajen karya gida da sata.
Hedikwatar ta ce an kara zafafa bincike don kama abokan aikin sa da ke tserewa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan ya cigaba da cewa; A wani aiki na daban da aka gudanar bisa bayanan sirri, jami’an Sashen Kazaure a ranar 23 ga Watan Yuni, 2026 da karfe 8:00 na dare sun yi awun gaba da kama kungiyar ‘yan satan baburori da safarar su a kan hanyar Dandi zuwa Kazaure.
An kama mutane hudu yayin da suke kokarin sayar da wani babur da ake zargi an sace.
Shugaban kungiyar an bayyana shi da suna Aminu Adamu, dan shekara 48, na Unguwar Galadanchi da ke Kazaure.
Bincike ya kara nuna cewa kungiyar na da hannu a satar babur da dama a yankin. A sakamakon haka, an samu dawo da babur guda hudu da aka sace.
Bayan kammala bincike, an gano cewa mutanen hudu suna da hannu a laifin kuma an gurfanar da su a gaban kotu mai hurmi don sauraren shari’a.
Akwai wani babban wanda ake nema da kuma wani abokin aikin sa da ke tserewa, kuma ana ci gaba da bincike domin kama su.
Da yake mayar da martani kan wannan ci gaba, mukaddashin kwamishinan yan sanda Attahiru Ahmad ya yaba wa jami’ai bisa gudanar da aiki cikin kwarewa, da hadin Kai da suka bayar wajen amsa sahihin bayanan sirri.
Ya sake nanata cewa rundunar ba za ta yarda da aikata laifi ba, kuma ta gargadi cewa Jihar Jigawa za ta ci gaba da zama wuri mara kyau ga masu aikata laifuka.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a da su hada kai da hukumomin tsaro ta hanyar ba da sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen hana laifi da kama masu laifin.
Hedikwatar ta tabbatar wa mazauna jihar cewa za ta ci gaba da sintiri da tattara bayanan sirri domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.










