Edita.
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa an kafa jam’iyyar APC ne a matsayin wata hanyar ta kawo sauyi a ƙasa, domin rage talauci, inganta tsaro da kuma farfaɗo da manyan cibiyoyi na gwamnati.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin babban taron jam’iyyar karo na huɗu da aka gudanar a Abuja, inda ya jaddada cewa APC ba kawai an kafa ta don cin zaɓe ba, sai dai a matsayin wata kafa da ke da burin gina Najeriya mai aiki da haɗin kai.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta kasance “gida ga duk wanda ke son ganin an gina ƙasa inda gwamnati ke aiki yadda ya kamata, tabbatar da tsaro da magance talauci kuma kowanne ɗan Najeriya ya rayu cikin mutunci da fata.”
Shugaban ya kuma tuna cewa an kafa APC shekaru 13 da suka gabata ne sakamakon haɗin gwiwar ƴan siyasa da suka haɗa kai domin ceto ƙasar daga matsalolin tattalin arziki a wancan lokaci, yana mai cewa har yanzu jam’iyyar na tsaye kan manufofin demokuraɗiyya da ke tabbatar da adalci, ci gaba da walwalar al’umma baki ɗaya.










