Daga Hassan R Jibrin.
Kotun Kolin Najeriya ta yanke hukunci akan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC.
Bisa doron hukuncin, Sanata David Mark,shine halastaccen shugaban jam’iyyar ta ADC ba abokin burmin sa ba Alhaji Nafi’u Bala Gombe.
Wannan hukuncin yasa kotun ta dawo da shari’ar dake gaban Babbar Kotu domin cigaba da sauraro.
Wannan hukuncin shine ya balle makatar duk wata kofar da INEC ta dogara da ita wajen soke sunayen shugabanin tsagin Sanata David Mark.










