YAKUBU UBA.
Ranar da ba zan taɓa mantawa da ita ba a rayuwa ta ita ce ranar da muka je wani ƙauye domin kai ɗauki amma muka dawo cikin wani yanayi da ya kusa zama na ƙarshe gare mu.
Mun tafi da nufin mu ceto rayuka, Mun san akwai haɗari, amma ba mu yi tsammanin irin abin da zai faru ba. Bayan mun isa, mun yi abin da ya dace, muka taimaka yadda ya kamata, muka kuma kuresu daga yan bindigan.
A lokacin, zuciyoyin sun cika da farin ciki mun ɗauka komai ya wuce. Amma ashe ba haka ba ne kwatsam a kan hanyar mu ta dawuwa ne komai ya sauya.
Ba zato ba tsammani, muka shiga tarkon da aka shirya mana kwanton ba una.
Hanya ta yi shiru, amma kafin mu ankara, sai harbe-harbe suka ɓarke daga kowane ɓangare.
A wannan lokaci ne mutum yake gane cewa rayuwa tana da ƙima fiye da komai.
Ba lokacin jarumtaka ta wofi ba ne, ba lokacin nuna ƙarfi ba ne, lokaci ne na tsira. Kowa ya shiga cikin shiri da tsari, muna neman yadda za mu fita daga wannan tarko cikin hikima.
Bugun zuciya ya ƙaru, hankali ya tashi, amma dole ne ka daidaita kanka idan kana son ka fita da rai.
Abin da ya ceci rayukanmu ba wai ƙarfin mu kaɗai ba ne, hadin kai ne, nutsuwa, da kuma sanin abin da ake yi a lokacin da ya dace.
Mun sha da kyar, amma Alhamdulillah, mun fita.
A yau idan na tuna, sai na gode wa Allah da wannan rana, domin da cikin sauƙi za mu iya zama labari kawai.Ga duk wanda yake ganin wannan lamari wasa ne, ko yana tunanin cewa zai iya tunkarar masu garkuwa da mutane ba tare da shiri ba to ka sake tunani.
Wannan abu ba wasa ba ne.
Allah ya kare mu baki ɗaya, ya tsare mana rayukanmu.










