Hassan Turaki.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kutsa gidan Sakataren karamar hukumar Kibiya ta jihar Kano, inda su kayi awun gaba da shi.
Shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Hon. Sabo Yusuf Usman ne ya shaida wa Guarantee Newspaper cewa lamarin ya faru ne ranar Juma’a da daddare a gidan sakataren da ke garin Dinya.
”Lamarin ya faru ne da ƙarfe 1:00 na dare, lokacin da sakataren ke bacci a gidan sa”, in ji shi.
Ya ci gaba da cewa lokacin da maharan suka zo sun tashi ɗan gidan sakataren da ke kwana a zauren waje, inda suka tilasta masa ƙwankwaso kofar gidan, sannan ya faɗa wa mahaifin sa cewa cikin sa na ciwo.
”Hakan kuwa aka yi, bayan ya ƙwanƙwasa mahaifin nasa ya ce wane ne? Sai ya ce shi ne (ɗansa), ya ce me ya faru? Sai ya ce cikin sa ne ke ciwo, nan take mahaifin ya buɗe ƙofa, daga nan maharan suka kama shi tare da ɗan nasa”, a cewar Hon Sabo.
Ya ƙara da cewa tuni dai jamai’an tsaro suka kai taimakon gaggawa, amma kafin zuwan su maharan sun tafi da sakataren bayan sun sako ɗan nasa.










