Daga Hassan Turaki.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ce Kudirin ‘Yan Sandan Jihohi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar ya kunshi kariya ta doka da na cibiyoyi da dama domin hana cin zarafin al’uma da amfani da jami’an tsaro ta fannin siyasa.Sanata Barau ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da yake amsa tambayar yan jarida cikin shirin _Hannu Da Yawa_, na gidan radio kaduna wanda tashar ta gabatar Kai tsaye kuma radio Nigeria Horizon FM Dutse ta sake yada wa masu sauraro a Jigawa da jihohin da ke makwabtaka da ita.A cewar sa, kudirin ya fito ne sakamakon tattaunawa da yawa da aka yi da Shugaban Kasa, Majalisar Dokoki ta Kasa, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, jami’an ‘yan sanda masu ritaya, gwamnoni, kungiyoyin farar hula, da jama’a.”Shugaba Tinubu ya binciki lamarin da kyau ya gano cewa yayin da mutane da yawa ke goyon bayan ‘Yan Sandan Jihohi, akwai tsoron cewa ana iya amfani da su wajen siyasa ko kuma nuna son kai na kabilanci. Shi ya sa aka saka kariya a cikin tsarin,” in ji shi.Da yake kawo misalin daya daga cikin kariyar, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya ce Shugaban Kasa yana da ikon kundin tsarin mulki na tsoma baki.”In an yi amfani da ‘Yan Sandan Jiha wajen tsoratar da mutane ko yin abubuwan da za su jefa rayuka da dukiya cikin haɗari, Shugaban Kasa yana da ikon kundin tsarin mulki na tsoma baki da umurtar ‘Yan Sandan Tarayya su karɓi alhakin,” in ji shi yayin da yake amsa tambayar wani mai kira daga jihar Sokoto.Sanata Barau, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa na sake fasalin kundin tsarin mulki, ya ce an gudanar da sauraren ra’ayoyin jama’a a yankuna shida na siyasa da kuma birnin tarayya Abuja domin magance damuwar jama’a.Ya bayyana cewa tsarin ya raba ayyuka a fili: ‘Yan Sandan Najeriya za su ci gaba da kula da laifukan kasa kamar ta’addanci da laifukan yanar gizo, yayin da ‘Yan Sandan Jiha za su mayar da hankali kan tsaron cikin gida da kiyaye doka da oda a matakin gida.Ya kara da cewa za a nada Manyan Kwamandojin ‘Yan Sandan Jiha ta hanyar tsari mai tsauri kuma doka za ta kare su daga shiga tsakani na siyasa. Ya kara da cewa kuma za’a dauki ‘yan sandan ne daga cikin al’ummomin su domin “sune suka san mutane, har ma da masu aikata laifi.”A kan batun kudi, Barau ya ce za’a tsara tsarin kudi da ka’idojin aiki yayin da ake ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulki da zartar da dokokin da suka dace.Sanatan ya bukaci Majalisun Dokokin Jihohi da su goyi bayan gyaran, inda ya bayyana sauyin a matsayin “mai ma’auni”, kuma mai matukar muhimmanci wajen sake tsara wani tsari na tsaron Najeriya.”‘Yan Sandan Jiha zasu inganta yadda muke magance satar mutane, garkuwa da mutane da sauran laifuka. Arewa zata amfana matuka.










