Hassan Turaki.
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, zai mayar da makarantar State Polytechnic Rural daga ƙaramar hukumar Rano zuwa ƙaramar hukumar Sumaila.
Matakin ya biyo bayan samun babbar makarantar Federal Polytechnic a ƙaramar hukumar Rano, domin samar da daidaito da bunƙasa harkar ilimi a sauran yankunan jihar.
Al’ummar Sumaila sun bayyana farin cikin su tare da gode wa Gwamna bisa wannan muhimmiyar gudunmawa da ake sa ran za ta taimaka wajen haɓaka ilimi, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin yankin.










