Daga Hassan R Jibrin.


Yayin da ake shirin fuskantar zaben 2027, APCn Kano mai rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar tara fara kirga asara domin Hon Sule Shu’aibu Shuwaki, Mamba mai wakiltar Karamar Hukumar Tudun-Wada, ya sanar da ficewarsa daga cikinta zuwa jam’iyyar PDP.


Shugaban Majalisar Dokokin, Rt Hon Isma’il Falgore, ya sanarwa zauren Majalisar a yayin zamanta na ranar Like a cewar sa “zamu yi kokarin lallashi ta hanyar tattaunawa da shi , domin ganin ya dawo,”

A cikin takardar barin APCn, Hon Shuwaki ya godewa tsohuwar jam’iyyar ta sa bisa damar da ta bashi, amma ya ce “bukatun al’ummar Tudun-Wada da nake wakilta, sune kan gaba’ A yanzu APC na da mambobi 37, NNPP 2, sai kuma PDP mai kujera 1 tilo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here