Daga Hassan R Jibrin
Kamar yadda Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa mahaddatan Al-Kur’ani Mai Tsarki 334 daga Kasashe 133 sun fara fafatawa a gasar karatun Al-Kur’ani da fassara a birnin Makkah.
Ita dai wannan gasar ta bana, itace karo na 46, mai lakabin “Gasar Sarki Abdu’azeez”, tana karkashin kulawar Sarki Salman Bn Abdul’azeez wanda ke kula da masallatan Haramaini guda biyu, na Madinah da Ka’abah.
Zunzurutun kudi Riyal Miliyan 10.2 daidai da Naira Biliyan 3.7 aka ware domin bayar da su a matsayin kyaututuka ga mahaddatan da suka yi bajinta a gasar.
Ma’aikatar Kula da Addini ta Kasar ta Saudiyya ke daukar nauyin da gudanar da gasar a duk shekara da nufin zabuwar da Kasashen Musulmai wajen kokarin haddar Al-Kur’ani da kuma fassarar sa.
Gasar an fara tane da nufin kammalawa a ranar 5 ga watan Rabi’u Awwal wanda tayi daidai da 19 ga watan Agusta.
A bana, an warewa mata wurinsu daban, sai dai zasu iya haduwa da tajwaririnsu maza a fafatawar karshe a birnin na Makkah.










