Mutumin Ya Hallaka Mijin Makwabciyar sa Saboda Zargin Neman Matar sa a Neja Wani lamari mai tayar da hankali ya faru a Jihar Neja, inda rundunar ‘yan sanda tayi nasarar cafke wani mutum mai suna Umar Audu mai shekaru 41 bisa zargin kashe makwabcin sa, Abubakar Muhammadu, mazaunin sansanin Fulani dake ƙauyen Wawa a New-Bussa, ƙaramar hukumar Borgu.

A cewar wanda ake zargin, marigayin ya daɗe yana neman soyayyar matarsa duk da cewa ya san tana da aure. Umar Audu ya ce matarsa ce ta fara sanar da shi lamarin, inda ya je ya gargadi Abubakar tare da tunasar da shi cewa matar aure ce.

Ya bayyana cewa bayan wani lokaci marigayin ya dakata, amma daga baya ya sake komawa. A cewarsa, ranar da lamarin ya faru, Abubakar ya samu lambar wayar matarsa tare da aika mata da saƙon soyayya.

Bayan matar ta sanar da shi, ya ɗauki adda ya nufi gidan marigayin, inda ake zargin ya kai masa hare-hare da suka yi sanadin mutuwarsa.Da aka tambaye shi dalilin aikata hakan bayan kama shi, Umar Audu ya ce:”Ban yi nadamar kashe shi ba.

Ya zaɓi ya mutu kamar kaza. Idan ya sake zuwa duniya, ba zai ƙara neman matar aure ba. A shirye nake in fuskanci duk hukuncin da doka ta tanada.

“Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, Muhammad Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, inda mutane da dama ke nuna alhini kan yadda rikicin da ya samo asali daga zargin neman matar aure ya kai ga rasa rai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here