Daga Hassan R Jibrin.

Rundunar Sojin Najeriya ta Bataliya 162 dake Mandaragirau Biu ia jihar Borno, ta sanar da gujewar Staff Sgt Idris Muhammed da wasu sojoji 103 daga bakin aiki bayan wani gumurzu da kungiyoyin Boko Haram da USWAP a ranar 2 ga watan Yuni na wannan shekarar.

Wata sanarwa da Laftana FI Ndubusi ya aikewa Hedikwatar Tsarro, ta bayyana cewa gudaddun sojojin na tare da makaman dake wurin su.Gujewar sojojin daga wuraren aikin ba karamin laifi bane a dokokin tsaron Najeriya.

Duk da manyan kudaden da gwamnati ke da’awar kashewa kan harkokin tsaron Kasa, har yanzu an kasa gane inda Gizon ke saka, musamman a yankin Arewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here