Daga Hassan R. Jibrin
Dandazon magoya bayan jam’iyyar NDC na garin Gano, Karamar Hukumar Dawakin Kudu, Jihar Kano, sun kai ziyara ta musamman ga tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar Dawakin Kudu/Warawa, Hon. Mustapha Bala Dawaki, wanda aka fi sani da “Maigidan Ruwa”
.Ziyarar ta biyo bayan sallamar sa daga Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, AKTH, bayan wata jinya da ya yi na tsawon makonni. Magoya bayan sun kai masa ziyar ne a gidansa da ke unguwar Na’ibawa domin jaddada goyon bayansu da yi masa addu’ar samun cikakkiyar lafiya.
Shugaban tawagar kuma Shugaban jam’iyyar NDC na mazabar Gano, Malam Mika’il Gidan Kuka, ne ya jagoranci tawagar. A jawabin sa, ya shaida wa Maigidan Ruwa cewa sun zo ne domin nuna masa cewa suna tare da shi a lokacin rashin lafiya da kuma bayan samun lafiya.
Ya ce addu’arsu ita ce Allah ya kara masa lafiya da karfin gwiwa wajen ci gaba da hidimar al’umma.
Da yake mayar da martani, Hon. Mustapha Bala Dawaki ya bayyana jin dadinsa da kuma godiya ga wannan ziyara ta musamman. Ya ce ya ji dadi da kuma kaduwa wajen ganin yadda magoya bayansa suka nuna damuwarsu da kaunarsu a lokacin da yake jinya.
Ya jaddada cewa alaka da ke tsakaninsa da al’ummar Dawakin Kudu/Warawa ta fi siyasa, domin ya dade yana yi wa mutanen yankin hidima ba tare da gajiyawa ba.Hon. Mustapha Bala ya wakilci mazabar a Majalisar Wakilai daga shekarar 2011 zuwa 2023.
Ya sha kaye a zaben 2023 a hannun Barrista Muhammad Hassan Danjuma na jam’iyyar NNPP.Duk da haka, magoya bayansa na ganin ya cancanci dawowa 2027.
Ana sa ran zai sake tsayawa takarar kujerar a zaben 2027 karkashin tutar jam’iyyar NDC.
Tawagar ta kammala ziyar da addu’o’i na neman Allah ya kara wa Maigidan Ruwa lafiya da albarka, tare da ba shi nasara a dukkan lamuransa na gaba.










